On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Gwamnatin Taraiyya Zata Kashe Naira Bilyan Biyu Domin Siyen Kayan Aiki Ga Jami'an Tsaro Dake Abuja

Kayayyakin Tsaro

Ministan Birnin taraiyya Abuja, Malam Mohammed Bello Yace sama da naira Bilyan Biyu ce gwamnatin taraiyya ta amince a kashe domin siyen motoci da kayan aiki na jami’an hukumomin tsaro dake birnin taraiyya Abuja, domin inganta sha’anin tsaro a Abuja da kewayenta.

A cewarsa sabbin motoci 60  masu dauke da tsarin manhajar sadarwa ta zamani  za’a siye su ne akan kudi sama da naira Milyan Dubu 1, kuma zasu dauki tsawon watanni biyu ne rak domin kawo su kasar nan.

Ministan birnin taraiyyar Abuja, ya kara da cewa, za’a siyawa  hukumomin tsaro kayan aiki daban daban akan kudi naira Milyan 847.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da ake sukar shugaban kasa Muhammadu Buhari dangane da amincewarsa  ta fitar da  naira Bilyan 1 da milyan  145 domin  siyawa jamhuriyar Nijar  motoci kirar Toyota Land Cruiser guda 10 domin inganta sha’anin tsaro.

Wani dan jarida mai bincike David Hundeyin ne ya bayyana a shafinsa na Twitter, inda yace  ya samu takarda daga ofishin kasafin kudi  na kasa  wadda ta nuna cewa shugaban kasar ya amince da siyan motocin.

Hundeyin ya kuma makala hoton takardar domin tabbatar da ikirarin cewa shugaban kasa ya amince da sakin kudin ga wani kamfani mai suna  Kaura Motors Nigeria Limited, a ranar 28 ga Fabrairun  2022.

Da take kare sayen motocin a ranar Larabar da ta gabata, ministar kudi, Zainab Ahmed ta ce an dauki wannan mataki ne domin baiwa kasar damar kare yankunanta  daga barazanar  tsaro  kamar  yadda aka saba yi a bisa al’ada.