On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Cibiyoyin Sauya Fasalin Ababen Hawa Zuwa Masu Amfani Da Gas

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da cibiyar sauya fasalin ababen hawa zuwa masu  amfani da iskar gas a babban birnin tarayya Abuja da Kaduna a hukumance.

Ta ce cibiyoyin za su bunkasa shirin amfani da gas samfurin CNG na gwamnati tare da rage tasirin cire tallafin man fetur ta hanyar rage farashin sufuri.

An bayyana hakan ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun ma’aikatar sufuri ta hannun  daraktan yada labarai da hulda da jama’a, Olujimi Oyetomi.

Ministan Sufuri, Said Alkali, da yake jawabi a wajen bikin, ya bayyana cewa, samar da makamashin da ya dace da muhalli kamar CNG zai taimaka wajen sake fasalin harkokin sufuri.

Haka kuma shirin Shugaban Kasa na fadada amfani da gas ya kaddamar da cibiyar sauya fasalin ababen hawa zuwa masu amfani da gas samfurin  CNG a Jihar Kaduna a wani bangare na kokarin Gwamnatin Tarayya na dakile radadin cire tallafin man fetur.

Da yake kaddamar da cibiyar a Kaduna, shugaban kwamitin shugaban kasa kan amfani da gas samfurin CNG, Zacch Adedeji, ya ce an tsara wurin  ne domin mayar da motoci masuaiki da  man fetur na yau da kullun zuwa motocin da ke amfani da iskar Gas.

Adedeji yace  cibiyar tana wakiltar kudurin Najeriya na komawa zuwa aiki da makamashi mafi saukin barazana da aminci da kuma sauki.

Shima da yake jawabi, Daraktan shirye-shiryen, na shirin  Michael Oluwagbemi, ya ce gasa samfurin CNG na da aminci kuma mai araha ne ga al'ummar Najeriya kuma zai samar da hanyoyin  makamashi mai tsafta da kare muhalli.