On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gwamnatinmu Zata Bada Fifiko Kan Bunkasa Ilimi Da Kiwon Lafiya - Abba Kabir Yusuf

Zababben gwamnan jihar Kano, Abba Kabiru Yusuf ya sha alwashin kammala dukkan ayyukan da aka yi watsi da su a jihar ta Kano.

A jawabinsa na samun nasarar zabe a daren jiya, Abba Kabir Yusuf, ya kuma yi alkawarin ba da fifiko kan ilimi da karfafawa da kuma bunkasa harkokin kasuwanci domin rage radadin talauci.

Zababben gwamnan ya ce gwamnatinsa za tayi koyi da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya kasance uban gidansa, inda ya yi alkawarin tabbatar da akidar Kwankwasiyya.

Ya kuma yabawa Kwankwaso bisa irin goyon bayansa, ya kuma godewa al’ummar Kano bisa gagarumin hadin kai da kauna da suka nuna masa duk da dimbin kalubalen da aka fuskanta a lokacin zabe.