On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Gwamnonin Sunce Basu Amince A Biya Kwararrun Da Suka Yi Aikin Dawo Da Kudaden Paris Club Ba

MALAMI DA KAYODE

A karo na biyu kungiyar gwamnoni ta kasa ta sake jaddada nuna rashin amincewarta da matakin da ministan shari’a na kasa Abubakar Malami SAN ya tsaya akai, wajen ganin an biya kwararrun da suka yi aikin dawo kudaden Paris Club hakkokinsu.

Shugaban Kungiyar na kasa,  Gwamna Kayode  Fayemi na jihar Ekiti, shine ya karanta  takardar bayan taron  gwamnonin ga manema Labarai na fadar shugaban kasa, a ranar Laraba jim kadan bayan kammala taron nasu da suka yi a Abuja.

A kwanan nan ne , Ministan shari’ar ya fadawa manema Labarai cewa kungiyar gwamnonin ta amince a biya kwararrun da suka yi aikin dawo da kudaden na Paris club wani kaso daga cikin kudaden.

To sai dai shugaban kungiyar  gwamnonin ya musanta kalaman da ministan yayi, Inda ya baiyana cewa zancen da ministan yayi na bogi ne, sannan kuma  ba shine matsayar da suke akai ba.