On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Har Yanzu Akwai Gibin Shinkafa Sama Da Tan Milliyan 2 A Najeriya - Bincike

Wani sabon rahoto da aka fitar ya nuna yadda ake cigaba da samun karuwar amfani da  shinkafa a kasar nan, al’amarin da ya sa ake samun gibin Shinkafara da kimanin tan miliyan biyu a duk shekara.

Wannan ya haifar da karuwar  sama da kashi 37 cikin 100 na farashin kayayyakin zuwa yanzu a cikin 2023, a cewar rahoton samar da amfanin gona na ‘AFEX kan  Kayayyakin amfanin gona na 2023.

A cikin rahoton ya zuwa yanzu, Najeriya ta kashe sama da dala biliyan 15 a cikin shekaru 10 da suka gabata domin cimma bukatar shinkafa duk kuwa da yuwuwar kasarnan zata na zama mai fitar da shinkafar kasashen waje.

Sai dai ana sa ran samun karuwar noman shinkafa da kusan kashi 4 cikin dari, sannan kuma za a kara samun karuwar farashin shinkafar da kusan kashi 32 cikin dari.