On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Har Yanzu Gwamnati Bata Biya Bukatunmu Ba - ASUU

Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da ikirarin gwamnatin tarayya na cewa ta biya kungiyar bukatunta.

Shugaban kungiyar ta ASUU a Jami’ar Ibadan, Farfesa Akinwole Ayoola, yace babu gaskiya ko kadan a ikirarin gwamnatin tarayya.

Kungiyar ta bayyana cewa har yanzu dukkan sassanta da suka fara yajin aikin na sama da watanni shida na kan bakarsu da yajin aiki, kuma sun jajirce wajen samun abin da jami’o’in gwamnati ke bukata daga gwamnati domin tsira da kuma gogayya da kasashen duniya.

Ya ce ya kamata ‘yan Najeriya su yi watsi da karyar da gwamnatin tarayya ke yi domin kuwa ikirarin da akeyi ya yi hannun riga da abunda yake a zahiri.

More from Labarai