On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Har Yanzu Tsugune Bata Kare Ba Kan Kiraye-Kirayen Ayu Ya Sauka Daga Shugabancin Jam'iyyar PDP Ta Najeriya

Da alama kiraye-kirayen da ake yi na neman shugaban jam’iyyar PDP, Iyorchia Ayu ya yi murabus ba zasu kare nan kusa ba.

A wannan karon, dan takarar Sanata a jam’iyyar a jihar Ondo, Ifedayo Adedipe, yana son Ayu ya ajiye mukaminsa domin masalahar jam’iyyar.

Gwamna Nyesom Wike na Rivers da wasu gwamnoni hudu sun yi ta kiraye-kirayen neman da ya yi murabus a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa domin tafiyar bai daya da kowa da kowa a harkokin jam’iyyar.

Da yake kara tsokaci a birnin Akure, Adedipe yace rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar ba al’amari ne na kashin kai ba tsakanin Wike da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar.

‘Dan takarar Sanatan na PDP ya ce abin da gwamnonin ke nema shi ne hana samun  dan takarar shugaban kasa da shugaban jam’iyyar na kasa su fito daga yanki daya.

More from Labarai