On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Haramcin Amfani Da Wayar Sailula A Shingen Dangwala Kuri'a Yana Nan Daram - INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC  ta ce haramcin amfani da  wayoyin hannu  a shingen dangwala kuri’a na nan daram.

Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa MahmoodYakubu shine ya bayyana haka a taron masu ruwa da tsaki na hukumar kan yadda za a magance tasirin kudi a babban zaben 2023 a Abuja.

Yakubu ya tabbatarwa da jama’a cewa INEC za ta cigaba da samar da matakan dakile barazanar sayen kuri’u, inda ya kara da cewa amincin hukumar zai cigaba da kasancewa tare da ‘yan kasa.

INEC ta ci gaba da cewa ta yi amfani da fasahohin zamani don tabbatar da sahihin tsari a babban zaben 2023.

A wani bangaren kuwa,  INEC ta amince da cewa ci gaba da kai hare-hare a ofisoshinta da sauran cibiyoyinta na yin barazana ga nasarar gudanar da zabukan 2023.

Hukumar zaben ta kuma koka kan yadda kokarin da akayi  a baya na hana sayen kuri’u ya ci tura, inda ta kara da cewa matsalolin na iya kawo cikas ga gudanar da zabe.

Shugaban hukumar ta INEC, Mahmood Yakubu shine ya bayyana damuwarsa a wasu taruka biyu daban-daban da aka gudanar a Abuja ranar Litinin a wani bangare na shirye-shiryen zaben.

Yakubu ya ce idan aka ci gaba da kai hare-hare har zuwa shekara mai zuwa, za su iya kawo cikas ga nasarar gudanar da zaben.

Ya kara da cewa idan har rashin tsaro a wasu sassan kasar bai gushe ba; zai iya shafar damar 'yan takara na samun adadin kuri'un da kundin tsarin mulkin kasa ya ayyana a matsayin wanda ya yi nasara.