On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Hauhawar Farashin Kayayyaki A Najeriya Ya Karu Zuwa Kashi 20.77 - NBS

Hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya karu a cikin wata takwas a jere, inda ya kai sabon matsayi da aka jima ba’a fuskanta ba tun shekaru 17 baya, a cewar bayanai daga Hukumar Kididdiga ta Kasa.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da farashin kayan abinci da makamashi ke kara hauhawa, da kuma ci gaba da faduwar darajar Naira.

A cewar rahoton NBS, hauhawar farashin kayayyaki ya karu zuwa kashi 20.77 a watan Satumba daga kashi 20.52 da aka samu a watan Agusta, mafi girma tun 2005.

Karuwar  farashin kayan abinci ya karu da kashi 23.34 bisa ɗari duk shekara idan aka kwatanta da kashi 23.1 a watan Agusta, yayin da ainihin hauhawar farashin kayayyaki ya ƙaru zuwa kashi 17.6 cikin ɗari a watan Satumba daga kashi 17.2 a watan Agusta.