On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Hisbah Zata Daidaita Yadda Ake Amfani Da Shafukan Sada Zumunta

Hukumar Hisba ta Jihar Kano Hadin gwiwa da Hukumar Tace Fina-fina da ‘Dab’i ta jihar Kano, Suna fara wani Yunkuri na tsaftace yadda ake tafiyar da harkokin shafukan sada zumunta a jihar Kano.

Shugaban Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta jihar Kano, Na’abba Afakallah ne ya baiyyana haka yayin hirarsa da manema Labarai, Ya kara da cewa duk da kasancewar  babban aikin hukumarsa ya ta’allaka ne akan harkokin Films, To sai Shafukan Sada Zumunta musamman shafin nan na Tik Tiko, Ya bawa wasu masu amfani dashi damar yin wasu abubuwa na rashin ‘Da’a a shafin.

Afakalla yace Hukumar tare da Hukumar Hisba sun kafa wani kwamiti wanda zai samar da wani tsare na magance wannan matsala, inda ya baiyana Dandalin TikTiko a matsayin wani waje  na  haddasa mutuwar aure da sauran cututtukan da suka shafi zamantakewa.

Kazalika ya baiyana takaicinsa dangane da yadda shafukan sada zumunta wadanda aka samar dasu domin nishadantarwa da kuma  isar da sakwanni masu amfani , amma a halin yanzu mutane  suka  sauya hanyoyin amfani dasu zuwa wasu abubuwa na rashin dacewa.

Afakalla yayi kira ga Iyaye dasu binciki yadda Yaransu ke gudanar da al’amuransu a shafukan sada zumunta  domin ganin basu kauce hanya ba.