On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Hukumar NAFDAC ta kama katan sama da 250 na gurbattun lemukan sha a Kano

Idan za’a iya tunawa dai a watan Ramadan na bara ne...

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC a jihar Kano ta kama wasu mutane 3 tare da kwace katan dari da hamsin na lemukan sha da hukumar ta bayyana a matsayin wanda aka samar ba bisa ka’ida ba.

An kwace lemukan  daga hannun wani Garba Yahaya na unguwar Kwana hudu Brigade wanda ake  zargi da samar da lemun tare da rarraba shi ta hanyar da bata dace ba. 

Idan za’a iya tunawa dai a watan Ramadan na bara ne akayi fama da gurbatattun lemukan sha a jihar Kano, wanda har suka yi sanadiyyar ajalin akalla mutane 10, yayin da kuma aka kwantar da daruruwan mutane  a asibiti, wanda daga bisani kuma wasu daga cikin su suka samu matsalar qoda a sakamakon shan lemun. 

Jami’in  hukumar ta NAFDAC Shaba Mohammed, wanda ya sanar da hakan ga manema labarai a  jihar Kano, yace anyi kamen ne biyo bayan kama wasu mutane 3 da ake zargi da saida gurbatattun lemukan sha ga alummar jihar.