On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Hukumar DSS Ta Bukaci A Kwantar Da Hankula Bayan Gargadin Kasashen Amurka Da Burtaniya A Najeriya

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta bukaci ‘yan Najeriya su kwantar da hankulansu biyo bayan wata sanarwar da Offishin jakadancin Amurka a Abuja ya fitar kan yiwuwar kai hari a wasu sassan Najeriya.

A wata sanarwa da mai magana da yawunta Peter Afunaya ya fitar, DSS ta shawarci ‘yan Najeriya su kasance cikin taka tsan-tsan. Haka kuma hukumar ta sha alawashin hada kai da sauran hukumomin tsaro domi yin duk mai yiwuwa wajen samun dorewar zaman lafiya.

DSS tace babu wani sabon abu a tattare da sanarwar gargadi da Amurka ke fitarwa.

Sai dai an buykaci ‘yan Najeriya su kasance masu bada cikakkun bayanai ga hukumar kan abubuwan da suka shafi duk wata barazanar ta’adanci a yankunansu.