On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Hukumar KEDCO Ta Dora Alhakin Karancin Wutar Lantarki Akan Masu Satar Wuta

Hukumar KEDCO

Biyo bayan korafe-korafe kan karancin samun wutar Lantarki daga al’umar jihar kano, kamfanin rarraba wutar Lantarki ta jiha KEDCO, ya Dora alhakin al’amarin akan yadda wasu ke hada wutar lantarkin ta barauniyar hanya da kuma lalata kayayyakin wutar da wasu ke yi a wasu bangarorin.

A cewar  kamfanin, irin  wannan  matsaloli ke haifar  da  Gobara  da  jan  wuta  da kuma katsewar  wutar  a  fadin  jiha.

Hakan  dai  na  kunshe  ne  cikin  wata  sanarwa  da  shugaba   sashen  yada  labarai  da  hulda  da  jama’a  na  kamfanin KEDCO, Ibrahim  sani  shawai,  ya  sanyawa hannu aka kuma aiko da kwapin ta nan Arewa Radio.

Daga  nan  kamfanin  na KEDCO  ya  bukaci  abokan  Hulda dasu   dauki  Gabarar  kare  kayyakin   Lantarki a yankunan su.

Sanarwar ta kuma kara da cewa, a wani sako da ya fitar, shugaban kamfanin KEDCO a nan Kano, Dr. Jamil Isyaku Gwamna, ya bukaci jama’a da su kasance masu alkinta kayayyakin wutar lantarki a mazaunan su, wanda hakan ne zai bada damar inganta samar da ita.

Daga nan sai ya yabawa al’umomin dake kokarin kai karar bata gari akan al’amuran satar wutar lantarki.