On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Hukumar Kula Da Yanayi Tayi Hasashen Samun Hazo Da Kura A 'Yan Kwanaki Masu Zuwa.

Hukumar kula da yanayi ta kasa ta baiyana cewar za’a fuskanci karuwar Hazo da kuma ‘kura wanda zai iya haddasa rashin gani sosai a ‘yan kwanaki masu zuwa

Hukumar  ta baiyana haka ne ta cikin wata sanarwa  mai dauke dasa  hannun shugabanta  Muntari  Yusuf Ibrahim, wadda aka fitar  jiya a Abuja.

Ta baiyana cewar  za’a fuskanci kadawar iska  mai karfi  da tashin kura a wasu bangarori na kasar nan musamman jihohin katsina da kano da Nguru  da jigawa  da Fotiskuma   da kuma Maiduguri  nan da  sa’oi  24 masu  zuwa.

Daga nan sanarwar ta bukaci jama’a dasu  daukin matakan kula da lafiyarsu da kuma yin tuki cikin natsuwa  ga masu ababen hawa.