On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Hukumar NDLEA Ta Bankado Miyagun Kwayoyi Da Ake Shirin Fitarwa Kasashen Duniya

Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA sun bankado wasu haramtattun kayyaki da ake yunkurin fitarwa zuwa kasashen Turai da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Asiya.

Da yake bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya ce haramtattun abubuwan da aka kama sun hada da nau’o’in kwayoyi a cikin sabbin wando na jeans da  kwalin sabulun gida da kwalayen abun sha.

Da yake tabbatar da cewa  an gudanar da aikin ne a Legas, ya ce daga cikin kayayyakin da aka kama sun hada da tramadol  da aka boye a cikin sabbin wando na jeans da ke kan hanyar zuwa kasar Cyprus da kuma jigilar tabar wiwi da aka boye zuwa Dubai.

Wasu kuma na kan hanyar zuwa Hong Kong,  da kuma jigilar wani haramtaccen abu da ya fito daga Florida a  Amurka.