On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Tace Zata Yi Adalci A Zabe Mai Zuwa

FARFESA MAHMOUD YAKUB

Hukumar Zabe ta kasa Mai Zaman Kanta INEC ta ce duk da cewar akwai babban kalubale wajen gudanar da babban zaben shekara mai zuwa, to amma hukumar zata tabbatar da anyi adalci a zaben.

Shugaban Hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu  shine  ya bayyana haka a  yayin bude wani taron karawa juna sani da aka shirya, domin sake yin nazari kan yadda aka gudanar da zaben gwamnonin jihohin Ekiti da Osun a birnin Ikko.

Farfesa Yakubu ya ce, Al’ummar kasar nan suna da kyakykyawan tsammanin cewa hukumar  zata dore da nasarorin da samu a yayin zaben gwamnoni na kwanakin baya da aka gudanar.

Mahmood Yakubu

SHUGABAN HUKUMAR ZABE TA KASA

A cewarsa, bayan nasarar da hukumar ta samu a zaben gwamnan Ekiti da aka yi, wasu mutane sun yi tsammanin ko hukumar ba zata iya samun irin wannan nasara ba a zaben gwamnan jihar Osun saboda tafi Ekiti girma, Sai gashi nasarar data hukumar ta zarta ta zaben jihar Ekiti.