On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Hukumar Zabe Ta kasa Mai Zaman Kanta Ta Fara Daukar Ma'aikatan Zaben 2023

Ma'aikacin Zabe

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar da fara daukar ma’aikatan zabe da zasu yi aiki a zaben shekarar 2023.

Hukumar ta kara da cewa ta bude shafin ta na internet don daukar ma’aikatan, tana mai kira ga alummar kasa dasu je su fara neman aikin.

INEC ta sanar da hakan ne ta cikin wani sako data wallafa a shafin ta na Facebook a yau laraba. Tace shafin nata wanda ta bude a yau za’a rufe shi a ranar 30 ga watan Nuwambar shekarar nan da muke ciki.

Za’a fara gudanar da gangamin zaben shekarar 2023 ne a karshen wannan wata da muke ciki.

More from Labarai