On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Hukumar Zabe Ta Mayar Da Martani Kan Hukuncin Hana Ta Dakatar Da Rijistar Katin Zabe

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta mayar da martani kan hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke game da hana hukumar dakatar da aikin rajistar masu zabe gabanin babban zaben shekarar 2023 dake tafe.

A ranar Litinin ne,  Mai shari’a Mobolaji Olajuwon ya dakatar da hukumar zabe daga kawo karshen  aikin rijistar katin zabe a ranar  30 ga watan Yuni. Alkalin ya bayar da umarnin ne a lokacin da yake yanke hukunci kan karar da kungiyar SERAP ta shigar a gabanta.

Kwamishinan Hukumar zabe kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, Festus Okoye, A yayin wata hira da aka yi dashi a shirin siyasa  na gidan Talabijin na Channels,Yaga baiken hukuncin da Kotun ta zartar Wanda yace  hakan zai shafi  aiyukan hukumar.

Ya kara da cewa hukuncin kotun ya saba da tsarin gudanar da rijistar katin zabe da hukumar  ta  shirya tun da farko.