On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Hukumar Zabe Ta Mayarwa Mawaki Davido Martani

SHUGABAN HUKUMAR ZABE DA MAWAKI DAVIDO

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta caccaki fitaccen mawakinan , Davido, wanda ya kasance ‘Da ga Dan uwan zababben gwamnan jihar Osun, Sanata, Ademola Adeleke, kan wa’adin da ya bawa hukumar zabe, akan ta tabbatar ta bawa kawunsa Adeleke takardar shaidar lashe zabe.

Sanata Adeleke na jam’iyyar PDP ya doke gwamna mai ci Adegboyega Oyetola na jam’iyyar APC  wadda ke yin mulki a jihar.

Idan ba’a manta ba, Mawaki  Davido ya tuhumi Hukumar zaben ta kasa mai zaman kanta, akan dalilan da yasa ta ki mikawa kawun  nasa, takardar  shaidar lashe zabe  bayan sa’o’i 48 kamar yadda doka ta tanada.

Da yake mayar da martani ta cikin wata sanarwa da  hukumar a zaben ta fitar,  shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu  yin zabe  na Hukumar  Festus Okoye, Ya baiyana cewa  hukumar nada  wa’adin kwanaki 14 domin bawa wanda ya samu nasara a kowane irin zabe  takardar  shaidar samun nasara.

More from Labarai