On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Ibrahim Bendel Ya Sake Shiga Hannun Hukumar NDLEA

Shekaru bakwai bayan ya tsere daga gidan yari bayan samunsa da laifin safarar miyagun kwayoyi, wani kasurgumin mai rarraba miyagun kwayoyi a babban birnin tarayya Abuja, Ibrahim Momoh, wanda aka fi sani da Ibrahim Bendel,  ya sake shiga hannun hukumar NDLEA a mafakarsa dake  Filin Dabo a  yankin Dei-Dei.

An fara kama Ibrahim Momoh ne a ranar 27 ga Nuwamba na shekarar  2014 da tabar wiwi mai nauyin kilogiram dubu 385 da digo 1, an gurfanar da shi a gaban kuliya, aka yanke masa hukuncin daurin shekaru bakwai da rabi a ranar 22 ga Yuli, na shekarar 2015. Sai dai a lokacin da yake zaman gidan yari a Kuje, ya tsere ranar 16 ga watan Mayu na 2016.

Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya bayyana hakan a karshen mako, inda ya ce, biyo bayan bayanan sirri, jami’an NDLEA a ranar 20 ga watan Nuwamba na 2022, sun kai farmaki ma’ajiyar tsohon mai laifin, Ibrahim Momoh, tare da gano buhunan tabar wiwi guda  dubu 81 da 81 mai nauyin kilogiram 1,278.

Yace Farautar tayi nasara a ranar 5 ga watan Nuwamba na 2023 lokacin da jami’an tsaro suka sake kai farmaki a maboyarsa da ke Filin Dabo, a unguwar Dei-Dei a Abuja, inda aka kama shi da kilogiram 56.9 na tabar wiwi da kuma gram 42.7 na Diazepam.