On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

INEC Ta Amince Da Sunayen ‘Yan Takarar Gwamna A Jahohin Kogi, Bayelsa Da Imo.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta amince da jerin sunayen ‘yan takara na karshe na zaben gwamna da za’a gudanar a jihohin Bayelsa da Imo da kuma Kogi a ranar 11 ga watan Nuwamba.

Kwamishinan yada labarai na INEC na kasa, Festus Okoye, a wata sanarwa da ya fitar ya ce amincewar ta yi daidai da tanadin dokar zabe da ke bukatar a fitar da jerin sunayen, kwanaki 150 kafin ranar zabe.

Okoye ya ce jerin sunayen na karshe da hukumar ta wallafa a shafinta na Internet ya nuna jam’iyyun siyasa 18 ne suka tsayar da ‘yan takara a Kogi sai  17 a Imo da 16 a Bayelsa.

Ya kara da cewa za a fara yakin neman zaben a hukumance a ranar 14 ga watan Yuni zuwa ranar 9 ga watan Nuwamba, don haka ya shawarci jam’iyyun siyasa da su kauracewa rigingimu su gudanar da harkokinsu  cikin lumana.