On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Iyorchia Ayu Ya Jagoranci Taron Gaggawa Na Kwamitin Gudanarwa Na Jam'iyyar PDP

Mako guda da dawowa daga daga duba lafiyarsa, shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, a ranar Talata, ya jagoranci wani gagarumin taron kwamitin gudanarwa na jam'iyyar na kasa.

Wani jami’in jam’iyyar na kasa, Timothy Osadolor ya shaidawa manema labarai cewa mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa shiyyar kudu Taofeek Arapaja da shugaban Kudu maso Kudu Dan Orbih, da mataimakiyar Shugaban jam’iyyar a Kasa, daga Kudu-Kudu Stella Effah-Attoe duk sun hallaci taron na  gaggawa.

Idan za a iya tunawa, a makon da ya gabata, Arapaja da wasu shugabanni  biyar sun mayarwa jam’iyyar kudaden hayar Naira milliyan 122 da dubu dari 4 da aka tura musu  ta asusun ajiyar banki, inda suka nuna shakku kan ikon Ayu na amincewa da irin wadannan kudade.

Sun yi zargin cewa sun samu shigowar  Kudi daga banki ne bayan sun gano akwai sama da naiara billiyan 10 na jam’iyyar amatsayin  kudin sayar da Form din takara a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Kwamitin gudanarwar ya yanke shawarar bincikar zargin cewa kudaden da aka turawa  mambobin kwamitin  cin hanci ne saboda Ayu yana da ikon iya amincewa da sakin Naira milliyan 10 ne kawai.

Jam’iyyar ta ba da umarnin gudanar da binciken cikin mako guda.