On Air Now

ZANGON SAFIYAR LAHADI

5:00am - Noon

JAMB Ta Tsawaita Wa'adin Rajistar Jarabawar UTME A Najeriya

Hukumar da ke shirya Jarrabawar shiga Jami’oi da sauran makarantun gaba da gakandire a Najeriya JAMB ta ƙara wa'adin rajistar jarrabawar UTME ta shekarar 2023 zuwa mako ɗaya.

Hukumar ta ce ta ƙara wa'adin ne saboda wahalhalun da ɗalibai ke fuskanta wajen samun kuɗin rajistar, da kuma matsalolin amfanin da tsarin banki ta internet wajen sayen lambobin rajistar ta Internet.

JAMB ɗin ta ce za a ci gaba da sayar da Form din har zuwa ranar Litinin, yayin da rajistar za ta ci gaba har zuwa ranar Laraba 22 ga watan Fabrairun da muke ciki.

Tun da farko dai hukumar ta JAMB ta sanya ranar 14 ga watan na Fabrairun a matsayin ranar da za ta rufe yin rajistar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Dakta Fabian Benjamin ya fitar ya ce zuwa ranar Talata an  t samu mutum milliyan 1 da 527 da 68 da suka yi rajistar jarrabawar, ciki har da ɗalibai dubu 168 da 748 da suka nuna sha'awarsu ta yin jarrabawar gwaji ta UTME.

Ya ƙara da cewa hukumar ta a yanzu  tana  yi wa mutum dubu 100 rajista a kowacce rana.