On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Jami'an Tsaro Na Iya Kokarinsu Wajen Bada Kariya Ga Mazauna Najeriya - Minista

Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a na kasa, Alhaji Mohammed Idris ya ce Najeriya na da aminci kuma kofa a bude take ga masu zuba  hannun jari na kasashen waje da masu yawon bude ido don gano damarmaki da zasu amfana.

Idris ya bayyana haka ne a jawabinsa a wani taron tattaunawa da manyan editoci da shugabannin gudanarwa na kafafen yada labarai ranar Litinin a Abuja.

Idan za’a iya tunawa a ranar 3 ga Nuwamba, Ofishin Jakadancin Amurka ya ba da sanarwar nuna damuwa da kumagargadi kan karuwar barazana a manyan otal-otal dake  manyan biranen Najeriya.

Sai dai Idris ya ce dukkan kasashen duniya suna da kalubale wanda ka iya zama cikas ga tattalin arziki, siyasa, da zamantakewa, ko al'adu.

Ya yi nuni da cewa, jami’an tsaro suna  iya bakin kokarinsu wajen ganin an kare lafiyar ‘yan Najeriya da mazauna cikinta baki daya.