On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Jami'an Tsaro Sun Kai Sumame Maboyar 'Yan Kungiyar IPOB

IPOB

Rundunar Yansandan Jihar Ebonyi Ta tabbatar da kai sumame Sansanin kungiyar tsaro ta yankin Kudu maso gabashin kasar nan wadda ta kasance reshen kungiyar IPOB, A Kauyen Oriuzor dake cikin karamar Hukumar Ezza ta Arewa, Inda ta samu nasarar halaka Mutum Daya tare da Dakume wani 1.

Kakakin Rundunar  Yansandan jihar, SP Chiris Anyanwu ne ya baiyana haka ta cikin wata sanarwa da aka fitar a birin Abakaliki, wadda kuma aka rabawa Manema Labarai a ranar Juma’a.

 

Yace Dakarun Kungiyar tsaron sun budewa Jami’ansu wuta a lokacin da suka hango su, wanda hakan ya haddasa musayar wuta a tsakaninsu, al’amarin da yayi sanadin halaka daya daga cikinsu mai suna Elijah, sannan kuma wasu 6 suka arce da harbin bindiga.

 

Ya kara da cewa mutumin da aka kama a lokacin  shine  Chibundu Ali dan asalin  yankin Ezzama wanda a yanzu haka yana a komarsu.

 

More from Labarai