On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Jami'an Yansanda Sun Halaka 'Yan Ta'adda Masu Yawa A Jihar Katsina

Yan Ta'adda

Rahotanni na baiyana cewa an halaka yan ta’adda da dama yayin da wasu suka jikkata a ranar Litinin, Bayan da jami’an yansanda suka dakile wani hari da suka yi niyyar kaiwa garuruwan Dadawa da Barkiya dake cikin karamar Hukumar Kurfi ta jihar Katsina.

A yayin artabu da yan ta’addar, Jami’an yansanda sun samu nasarar kwato Tumaki 74 da Awaki 34 da kuma Shanu Biyu, kamar yadda kakakin yansandna jihar SP Gambo Isah ya baiyana.

Yace  sakamakon kiran neman dauki da suka samu da karfe 1 da rabi na dare, kana cewar  Yan bindigar wanda yawan ya kai 80 akan Babura sun fara afkawa yakunan, hakan tasa suka yi gaggawar zuwa wajen tare da dakile yunkurin nasu.

Ya kara da cewa har yanzu  jami’an rundunar  sun yiwa  yankunan kawanya domin  cafko yan ta’addar da suka ji raunika  sannan kuma sun dauke gawarwarkin wadanda aka halaka.

More from Labarai