On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Jami'ar Ahmadu Bello Dake Zariya Zata Koma Bakin Aiki Ranar 24 Ga Watan October

KOFAR SHIGA JAMI'AR AHMADU BELLO DAKE ZARIA

Shugabancin jami’ar Ahmadu Bello dake zari’a a jihar Kaduna, ta bayyana ranar litinin 24 ga watan October nan da muke ciki a matsayin ranar da zata koma harkokin koyo da koyarwa.

Jami’in hulda da jama’a na jami’ar Malam Auwal Umar, wanda ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da aka fitar  zaria a yau, yace komawa bakin aikin ya biyo bayan dakatar da yajin aikin watanni 8 da kungiyar ASUU ta gudanar.

Umar yace majalisar kolin jami’ar ta amince ta koma harkokin koyo da koyarwa a wata ganawar gaggawa data yi.

Yace majalisar kolin jami’ar ta kuma amince da kalandar karatu ta shekarar 2021 da shekarar 2022 da akayi wa gyara.