On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Jami'ar Bayero Ta Baiyana Dalilan Da Suka Sanya Karin Kudin Makaranta

BUK

Jami’ar Bayero ta kare matsayar data dauka na kara kudin makaranta, Inda ta baiyana cewar karin ba shi da wata alaka da janye tallafin mai ko kuma baiwa dalibai lamunin Karatu.

Idan ba’a manta ba, A cikin mujallar  dajami’ar ke wallafawa ta musamman,Mukaddashiyar  Magatakardar jami’ar, Amina Umar Abdullahi, ta bada sanarwar  yin karin kudin makarantar da kaso 100 bisa 100,  ga masu karatun digiri da kuma  babban digiri.

A yayin hirarsa da Arewa Radiyo, Kakakin jami’ar, Lamara Garba,  Ya ce karin kudin makarantar na da alaka da umarnin da gwamnati  mai ci  ta baiwa manyana makarantu a kasar nan, kan cewar su nemi hanyoyin samun kudin shiga.

Sai  dai   ya  ce duk da karin kudin makarantar  wani babban nauyi ne  ga  dalibai, To sai dai kuma har  yanzu, najeriya na cikin jerin kasashe masu saukin biyan kudin makaranta.

masu karatu a bangaren likitanci da sauran darussan kimiyya zasu rika biyan naira dubu 170 ga sabbin shiga  sai kuma  wadanda ke ciki zasu rika biyan naira dubu 160, yayin da sauran darussan zamantakewa, kamar  fannin shari'a, da nazarin addinin musulunci  za'a rika biyan naira dubu 97 ga  daliban dake cikin jami'ar, saiu kuma sabbi zasu rika biyan naira dubu 105