On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Jami'ar Bayero Zata Koma Bakin Aiki Daga Ranar Litinin 24 Ga Watan Octoba

KOFAR SHIGA JAMI'AR BAYERO DAKE KANO

Jami’ar Bayero dake nan Kano, ta baiyana cewa zata cigaba da harkokin koyo da koyarwa daga ranar 24 ga watan da muke ciki.

Wata sanarwa da Mataimakin Magatakardan jami’ar, Lamara  Garba , yace bayan taron da hukumar gudanarwar jami’ar ta yi a ranar 13 ga wata Octoban da muke ciki ne ta amince da lokacin da zata koma bakin aiki.

Sanarwar ta biyo bayan janye yajin aikin tsawon watanni takwas da kungiyar Malaman Jami’oi ta  kasa ASUU ta yi a ranar  Juma’ar  data  gabata.

A wani bangaren kuma, Wakilinmu Victore  Chiristopher  wanda ya kai ziyarar gani da ido zuwa jami’ar ta Bayero da kuma ta Yusuf Maitama Sule dake nan Kano, Yace har yanzu  Dakunan daukar darasi na jami’oin na a kulle.

Kazalika wakilin namu,Ya baiyana mana cewar,  Sabuwar  matsugunnin Jami’ar Bayero dake nan kano, Ya kasance  wayam, a yayin da ake saran Dalibai zasu koma makaranta kowane lokaci  daga  yanzu.