On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Jam'iyyar ANC A Afirka Ta Kudu Ta Shirya Zama Na Musamman Kan Makomar Shugaba Ramaphosa

Jam'iyya mai mulki a Afirka ta Kudu za ta ci gaba da tattaunawa yau lahadi kan makomar shugaba Cyril Ramaphosa, wanda ake zargi da wata badakala da ta jefa shugabancinsa cikin hadari, yayinda ake kara matsin lamba ga Ramaphosa ya ajiye aiki ko kuma a tilasta masa murabus.

Jam’iyyar ANC za ta yi wani zama na musamman na kwamitin zartarwa na kasa da  karfe  12 agogon kasar a yau lahadi.

Kwamitin ya gana a takaice a birnin Johannesburg a ranar Juma'a kafin ya shaidawa 'yan jarida cewa zai yi nazari sosai kan gaskiyar shari'ar da ake yi wa shugaban. Ramaphosa dai ya sha suka ne tun watan Yuni, lokacin da wani tsohon jami’in leken asiri ya shigar da kara gaban ‘yan sanda yana zarginsa da boye wani fashin da aka yi masa a watan Fabrairun 2020 a gonarsa da ke arewa maso gabashin Afirka ta Kudu daga hannun hukuma.

 Ramaphosa ya ce wasu makudan kudade da aka jibge a gonar, an biya su ne na bashin  wani dan kasuwa dan kasar Sudan.

Wannan badakalar dai ta haifar da da mai ido kan yunkurin Ramaphosa na bayyana kansa a matsayin wanda ba shi da hannu a cin hanci da rashawa bayan mulkin shugaba Jacob Zuma na cin hanci da rashawa.

 Kwamitin kwararru na  shari'a ya kammala cewa shugaban  yana da karar da zai amsa. Sai dai mai magana da yawun Mista Ramaphosa yace shugaban zai yi yaki da hakan kuma maimakon ya yi murabus zai nemi wa'adi na biyu a matsayin shugaban jam'iyyarsa ta African National Congress (ANC)..