On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Jam'iyyar APC Ta Bukaci Jam'iyyar PDP Data Kama Sabgar Dake Gabanta

PDP DA APC

Jam’iyyar APC mai mulkin kasa taja kunnen shugabancin Babbar Jam’iyyar Hamaiyya ta PDP akan ta mayar da hankalinta wajen warware rikicin cikin gida da ya dabaibaiye ta a maimakon bugewa da zargin juna da take yi.

Gargadin na zuwa ne kwanaki hudu, bayan da shugaban jam’iyyar PDP na kasa Sanata Iyorchiya Ayu ya zargi jam’iyya mai mulki da daukar nauyin masu wallafa labaran karya, domin rura wutar kan takun sakar dake tsakaninsa da  gwamnan jihar  Ribas Nyesom Wike.

Shugaban yayi wannan zargi ne ta cikin wata sanarwa da mashawarcinsa ta bangaren Yada Labarai , Simon Imobo Tswam ya fitar a ranar juma’a.

Da yake mayar da martani akan zargin, Sakataren Jam’iyyar APC na kasa, Felix Morka, Ya roki shugaban jam’iyyar na kasar Sanata Ayu, da ya fita daga harkokinsu tare da kama sabgar dake gabansa.