On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Jam'iyyar APC Ta Kaddamar Da Yakin Neman Zabenta Na Gwamna A Jihar Kano

Gangamin Yan Jam'iyyar APC a Gaya

Gabanin babban zaben shekarar 2023, jamiyyar APC mai mulki a jihar Kano ta kaddamar da yakin neman zabenta na gwamna a karamar hukumar Gaya.

Da yake jawabi  ga  magoya bayansa yayin bude  gangamin, dan takarar gwamana a jamiyyar Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ya jaddada  cika   alkawuran daya dauka  muddin aka zabe shi a shekarar 2023 

Wakilin mu na fadar gwamnatin jiha Abdurrahman Balarabe Isah, ya rawaito mana cewa gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bada tutocin jamiyyar ga yan takarar majalisar tarayya da kuma na jiha wadanda suka fito daga yanki.

Jamiyyar ta dakatar da mika tutar ga dan takarar kujerar gwamna, inda shugaban jamiyyar Abdullahi Abbas yace, za a mika tane yayin gangamin yakin neman zaben shugabancin kasa a nan  jihar Kano.

More from Labarai