On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Jam'iyyar APC Ta Mika Sunan Sanata Ahmed Lawan A Matsayin Dan Takararta Na Sanatan Yobe Ta Arewa.

Sanata Ahmed Lawan da Bashir Machina

Jam’iyyar APC mai mulkin kasa ta mika sunan Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Lawan Ahmad ga Hukumar zabe ta kasa a matsayin Dan takarar ta na sanata mai wakiltar Yobe ta arewa a zabe mai zuwa.

Wannan mataki ne na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da  Bashir Machina, wanda ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a zaben, ya dage  kan cewar ba zai janyewa  shugaban majalisar dattawan takarar ba.

Lawan wanda ya sha kaye a yayin zaben fidda  gwani na Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar  APC a hannun Bola Ahmed Tinubu bai shiga  zaben fidda gwani na sanata a mazabar Yobe ta Arewa ba.

Sai dai a nasa  bangaren, Machina  ya roki jam’iyyar APC da ta  shigar da sunan sa, kuma bashi da wani zabi da ya rage masa illa  ya nemi hakkinsa a gaban shari’a.

 

More from Labarai