On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Jam'iyyar APC Ta Soki Matakin Mamaye Gidajen Tsohon Gwamna Matawalle Na Jihar Zamfara

Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta yi Allah-wadai da kakkausar murya akan yadda jami’an ‘yan sandan jihar Zamfara da jami’an DSS suka mamaye gidajen tsohon gwamna Bello Matawalle dake Gusau da Maradun.

Acewar sanarwar da Yusuf Idris Gusau aakataren yada labarai na APC Jihar Zamfara ya fitar,  mamayewa ba bisa ka'ida ba, babban cin zarafi ne ga tanadin sashe na 34, 35, 37, 41, 42 da 43 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999. 

APC ta ce idan har gwamnati na ganin tana da wani zargi ko korafi kan  tsohon gwamna zai fi kyautuwa  a gurfanar da shi a gaban kotu maimakon yin amfani da irin wannan mataki.

Sanarwar ta yi kira ga ‘yan sanda da jami’an tsaro na farin kaya DSS da su gaggauta daukar kwararan matakai don dakile wannan barna da gwamnatin jihar Zamfara ke yi, kuma dole ne a gano wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da fuskantar  hukunci kan matakin da suka dauka. 

"Muna kira ga Sufeto Janar na ‘yan sanda da ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa tare da gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika ta haramtacciyar hanya ta kutsawa gidajen jagoran jam’iyyar APC na Jihar Zamfara  kuma tsohon Gwamna Bello Matawalle, Inji APC.

Yanzu haka dai ‘yan sanda sun kafa sansani da rufe hanyoyin zuwa gidan Matawalle  na Gusau kuma an girke ‘yan sanda a dukkan gidajen, acewar Yusuf.