On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Jam'iyyar NNPP Ta Baiyana Bukatar Atiku Abubakar Na Yin Sabuwar Maja A Matsayin Shan Magani Bayan Mutuwa

ATIKU

Manyan jam’iyyun hamaiyya na kasar sun fara mayar da martani kan kiran da ‘dan takarar shugaban kasa a zaben da ya gabata karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi, inda ya baiyana cewar kamata ya yi jam’iyyun Hamaiyyar su hade wuri daya domin karbe mulki daga hannun jam’iyyar APC.

Idan ba’a manta ba, Atiku Abubakar  ya baiyana bukatar  yin sabuwar Majar ne a yayin da ya karbi bakuncin shugabannin majalisar bada shawarwari a tsakanin jam’iyyu ta kasa a Abuja  ranar Talata.

A martanin da jam’iyyar  Labour  ta yi ta hannun mukaddashin sakataren yada labaranta Obiora Ifoh, Ya baiyana  yunkurin hadewar wuri daya a matsayin wani abu da ya d ace, wanda kuma ya kamata ayi nazari kansa.

Haka zalika itama jam’iyyar  NNPP ta hannun sakataren yada labaranta na kasa Yakubu Shendam, ya baiyana kiran da Atikun ya yi a matsayin abun jan hankali  sannan kuma magani ne bayan mutuwa.

Ya kara  da cewar  za’a yadda da bukatar Atikun ne kadai idan har zai goyi bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso  domin ya karbo mulki daga hannun jam’iyyar APC a shekarar  2027.