On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Jam'iyyar PDP Ta Lashe Zaben Gwamnan Jihar Osun

Sanata Ademola Adeleke

Sanata Adeleke Ademola na jam'iyyar PDP ya lashe zaben gwamnan jihar Sousna da aka yi a ranar Asabar.

 

An aiyana  Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben  gwamnan a hukumance.

Baturen zaben, farfesa Oluwatoyin Ogundipe, shine ya baiyana sakamakon zaben, wanda yace Adeleke ya samu kuri'a Dubu Dari Hudu da Ukku da Dari Ukku da Saba'in da Daya, yayin da gwamnan jihar Adegboyega Oyetola na jam'iyyar APC, ya samu kuri'a Dubu Dari 3 da 75 da guda 27

Ita kuwa jam'iyyar LP ta Peter Obi ta samu kuri'a Dubu 2 da 729 yayin da jam'iyyar NNPP ta sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta samu kuri'a 393.

A zaben gwamnan jihar ta Osun da jam'iyyu 15 suka fafata, Sanata Adeleke ya samu nasarar lashe kananan hukumomi 17 daga cikin 30 da ake dasu a jihar.

More from Labarai