On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Jam’iyyar PDP ta zargi APC da karkatar da dukiyar kasa wajen yakin neman zabe

Babbabr jam'iyyar adawa ta (PDP) ta zargi APC mai mulkin kasa da yin wakaci ka tashi da dukiyar kasa wajen yakin neman zabe

Jam’iyyar adaewa ta PDP ta zargi jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan, karkashin jagorancin shugaban kasa Mohammadu Buhari da yin amfani da dukiyar kasa wajen tara kudaden yakin neman zabe a shekarar 2023 mai zuwa.

Ta cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar Hon. Debo Ologunada ya fitar a ranar talata, jam’iyyar adawar ta yi zargin cewa APC na karkatar da kudaden da aka warewa ma’aikatu da hukumomin gwamnati, da na biyan ma’aikata albashi zuwa ga nau’ikan mutane daban-daban domin siyan fam din takara a karkashin jam’iyyar akan zunzurutun kudi miliyan 100.

Sanarwar tace: “jam’iyyar mu na sane da yadda ake dibar kudaden al’uma daga asusun hukumomi da ma’aikatun gwamnati, ake kuma bawa mutane da basu da dalilin samun kwatankwacin wadannan kudade domin siyen fam din tsayawa takarar shugaban kasa ga mutanen da ba za ma su iya cin zaben kananan hukumomi ba”.

“Muna bayanan sirri kan yadda wani babban jami’in jam’iyyar APC ke wa kaci ka tashi da dukuyar kasa, hadin baki da wasu manyan jami’an babban bankin kasa na CBN”.

Sanarwar ta kuma kara ada cewa, “idan yan Najeriya zasu iya tunawa, jam’iyyar mu ta PDP ta taba ankarar da al’umar kasa a baya kan yadda babban bankin kasa (CBN), karkashin jagorancin Godwin Emefiele, ya zama tamkar wani reshen harkokin kudi na jam’iyya mai mulki ta APC, inda suke fitar kudade ta hanyoyi mabanbanta da suka sabawa dokar kasa, wajen fitar da kudade domin amfanin jam’iyyar.

Jam’iyyar adawar ta yi kira ga hukumar yaki da masu yiwa tattalin aarzikin nkasa zagon kasa na EFCC, babban akanta na kasa, da babban mai binciken kudi na kasa da su fara gudanar da bincike akan wannan batu ba tare da wani bata lokaci ba, hadi da sa ido akan shige da ficen dukiyar kasa, musamman ma a wannan lokaci da ake shirye-shiryen zaben shekarar 2023 mai zuwa.

Ta kuma bukaci majalaisun dokokin kasar nan da su tabbatar ada cewa sun gudanar aiyukan su kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanada wajen bankadowa tare da tona asirin jami’an gwamnati da aka ka aka kama da hannu wajen wawure dukiyoyin al’uma.