On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Jam'iyyar PDP Tace Gwamna Wike Babban 'Dan Yatsa Ne A Cikinta

WIKE DA ATIKU

Sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Samuel Ayanwu, Yace gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike, Ya sadaukar da kansa matuka wajen samun dorewar cigaban jam’iyyar.

Ta cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin Owerri na jihar Imo a yau, kakakinsa, Ikenna Onuoha, Yace bai taba yin wasu kalamai na sukar  gwamna wike ba, dangane da rikicin ciki gida da jam’iyyar PDP ke ciki.

Sakataren jam’iyyar  PDP na kasa, Ya kara da cewa  rahotannin da wasu kafafen  yada Labarai suka wallafa, wanda kecewa ya nisanta kansa da gwamna wike basu da kanshin gaskiya a cikinsu, sai dai kawai an kirkire su ne domin haddasa rabuwar kawuna a tsakaninsu.

Sanarwar  ta kara da cewa, Mister Anyanwu ya umarci lauyoyinsa su  fara shirin daukar matakin shari’a akan wanda ya wallafa Labarin.

 

More from Labarai