On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Jam'iyyun Siyasa Sun Amince Da Yarjejeniyar Zaman Lafiya Gabanin Zaben Gwamna A Jihar Kogi

Gabanin zaben gwamnan jihar Kogi a ranar Asabar, jam’iyyun siyasa goma sha takwas da zasu fafata a zaben sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban kwamitin zaman lafiya na kasa, Janar Abdulsalam Abubakar mai ritaya, ya ja hankalin ‘yan takarar gwamna a jihar.

Abubakar, wanda  John Onaiyekan ya wakilta, ya ce ya fara nuna shakku sosai a kan jajircewar ‘yan takarar da ke cikin irin wannan yarjejeniyar zaman lafiya wajen biyayya ga alkawarin.

Sai dai ya bukaci jam’iyyun da su tabbatar sun yi biyayya ga yarjejeniyar a lokacin zabe.