On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Japan Ta Casa Jamus A Gasar Cin Kofin Duniya

WASAN JAMUS DA JAPAN

A yayin da kasashe ke cigaba da bada mamaki, kasar Japan ta doke kasar Jamus da ci 2 da 1, a wasan su na farko a gasar cin kofin duniya yau Laraba, kasar wadda ta lashe gasar har sau 4, kana kuma ta mamaye wasan a zangon farko kafin tafiya hutun rabin lokaci.

Kwallon su ta farko sun samu ne ta hannun dan wasa Ilkay Gundogan, yayin da ita kuma Japan dan wasa Ritsu Doa da kuma  Takuma Asano, suka jefa mata kwallayen ta a mintuna na 75 da kuma 82.

Kasar Jamus dai wadda na cikin wadanda ake saran za su lashe gasar, tana cikin rukunin E, kuma zata fafata wasanta  tare da kasar Spain da Costa Rica.

More from Labarai