On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Jigon Rahoton Mu Na Mako Akan Jarabawar Qualifying A Nan Kano

Daliban wata makarantar gwamnati a Kano

Tun da gwamnatin jihar Kano ta sanya jarabawar shiga ajin karshe a matsayin mizani na daukar nauyin daliban da zasu rubuta jarrabawar kammala karatun sakandare, a wancan lokacin abin da ake bukata shi ne dalibi ya yi nasara a darrusa 5 da suka hada da Turanci da lissafi.

Sannu a hankali, sai aka mayar da samun cancantar hakan  zuwa darrusa 7 kafin daga bisani ta daga darajar cancantar zuwa yin nasara a darrusa 9 a bana, kuma da dama daga daliban suka gaza samun wannan damar.

A Yanzu haka, iyayen daliban da suka gaza samun yin nasarar a dauki nauyin su,  ba wai kawai suna zargin gwamnati da gaza sauke nauyin da ya rataya a wuyanta  ba ne, sun koka dangane da lokacin da aka fitar da sakamakon, Wanda bai basu damar nemo kudin da zasu biyawa yaransu kudin ba.

Yayin da iyayen ke ci gaba da tofa albarkacin bakinsu, ’ya’yansu da abin ya shafa su ma sun bayyana irin tasu damuwar.

Guda daga cikin su yace, “akwai masu credit 7 zuwa 8 a cikin mu, saboda muna neman gwamnati taimaka domin kuwa rashin hakan ka iya sawa da yawa su hakura da karatun nasu”.

Wani kuma ya bayyana cewa, “gaskiya ban ji dadin wannan abun ba. Credit 8 na samu kuma zai yi wuya na cigaba da karatun.

A yayin da ake ci gaba da mayar da martani, Asiya Aliyu Garba, da ta Yi nasarar cin jarrabawar ta yaba wa gwamnati bisa wannan karanci  da ta yi mata. “a gaskiya naji dadin samun nasara da nayi da credit guda 9 kuma gwamnati ta biya mun kudin jarabawa, wanda ko shakka babu, hakan zai kara mun gwiwa.”

Shima, Umar Salisu, Wanda a halin yanzu yana aji biyu na babbar Makarantar sakandare  SS2, Kuma yana shirin rubuta jarabawar ta  shiga ajin karshe a shekara mai zuwa. Ya ce babu wani dalili na fargaba game da  jarrabawar ta cancanta, yace shi  yana ganin hakan zai sa shi ne ya kara himma. “Hakan zai sa lallai dalibai su rika dagewa wajen karatun su, sanin cewa ba za a biya musu ba idan suka gaza cin jarabawar.”

Da yake tsokaci kan wannan ci gaban, wani malami a kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi, Dokta Aminu Idris, ya nuna rashin jin dadinsa  kan irin yadda  iyaye ke kallon daukar nauyin jarrabawar  a matsayin hakki mai makon taimako.

Yace “wannan bai kamata ace muna ta korafi akan sa ba, mu me muka yi akai? Idan muka bar wa gwamnati komai, gaskiya abun ba zai yiwu ba, tirke yayan mu ya kamata mu yi, mu tursasa su akan karatun su, sannan mu yi tanadi akan jarabawar tasu tun da wuri.”

Da aka tuntubi Babbar Sakatariyar a ma’aikatar ilimi ta jiha, Hajiya Lauratu Ado Diso, ta danganta sabbin ka’idojin da Gwamnati ta sanya a matsayin hanyoyin inganta harkar ilimi a jihar nan. “Gwamnati ba cewa tayi ta wanke hannun ta akan harkar nan ba, kuma da aka ce 9 credit din nan gwamnati nan tana cigaba da kokari.” “Kuma kamata yayi iyaye su fahimci cewa ana shirya jarabawar ne ba wai dan gwamnati ta biya wa dalibai kudin jarabawar ba, ana yi ne don su san ya ma zasu rubuta jarabawar karshe ta makarantun sakandire ne.”

Da aka tambaye ta game da  rade-radin da aka yi na cewa an dauki matakin ne da gangan don rage yawan masu cin gajiyar daukar nauyin jarrabawar sakamakon kudin da ake kashewa, sai Diso ta bukaci masu ruwa da tsaki dasu tallafawa kokarin gwamnati na rage wahalhalun kudi da take kashewa a wannan fannin.