On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Jigon Rahoton Mu Na Wannan Mako Akan Ambaliyar Ruwa Da Ta Addabi Wasu Sassan Kano

Friday, 12 August 2022 19:31

By Abdulmumin Abubakar Abubakar Tsanyawa

Mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya na sa'o'i 48 da aka samu a wasu sassan jihar nan, a ranakun 2 da 3 ga watan Agusta, sai dai ya jawo gagarumar asara, data hada da asarar rayuka da dumbin dukiyoyi na miliyoyin naira.

A karamar hukumar Ajingi, wani gini da ya rushe sakamakon ruwan saman ya yi sanadiyyar mutuwar  ‘yar Dayyabu Abdullahi, Mai shekara 3 Kana, ibtila’in ya halaka Yarinyar Abufura Hudu ‘yar shekara 5. Kamar yadda suka shaidawa  Arewa Radio.

Kazalika a kauyen Gwanda dake karamar hukumar Dambatta, Wani mai shekaru 75, Malam Haruna Dahiru,  ya rasa matarsa ​​sakamakon mamakon ruwan sama. 

Ambaliyar ta raba Ai Mai Chasa,  mahaifiyar Mahaifiyar Marayu da gidanta, a Danbagina dake Karamar hukumar Dambatta,  yanzu haka sun sami matsuguni a makota. 

Mamakon ruwan ya shafi gidaje  346 a yankin Shuwawa da Danbagina, Inda a yanzu da dama ke rayuwa a wani fili da Dare suke nemi makwanci a gidajen 'yan uwa da abokan arziki.

Duk da gargadin da hukumar kula da yanayi ta Kasa  NIMET ta yi, Babban Sakataren Hukumar Ba da agajin gaggawa ta Jihar Kano, SEMA, Dokta Sale Aliyu Jili, ya ce hukumar ta samu adadin wadanda ambaliyar ruwa ta shafa  a bana, fiye da shekarar data gabata.

A cewarsa, yayin da ambaliyar ruwa ta lalata gidaje 3,337 a shekarar da ta gabata a nan Kano, rahoton wucin gadi na hukumar a bana ya nuna cewa mutane 9 ne suka mutu, kana 9 suka jikkata, yayin da gidaje 6,417 suka lalace.

Jili ya ce an yi kiyasin asarar da aka yi kan sama da Naira miliyan 541, sai dai hukumar ba ta da kayan agaji da za ta tallafa wa wadanda abin ya shafa duk da tsananin bukata hakan.

Lamarin ba wai garuruwan dake wajen Birnin Kano kadai ya yi shafa ba; Yawancin wurare masu mahimmanci a cikin  birni sun fuskanci ire-iren wannan matsalar ba, sakamakon rashin kyan hanya, da zubar da  shara ba bisa ka'ida ba da kuma rashin tsari na magudanar ruwa.

Da aka tuntubi Daraktan tsare-tsare da sa ido a ma’aikatar muhalli ta jihar, Dokta Garba Sale Ahmad ya bayyana rashin kula da muhalli da  kwadayi da rashin sanin matsalolin sauyin yanayi da ma matsalar dumamar yanayi a matsayin manyan dalilan dake haddasa ambaliyar ruwa.

Daga nan sai ya ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da wayar da kan jama’a kan tsaftar muhalli tare da daukar tsauraran matakai kan musu karya doka.

 

Mai Rahoto: Kamaluddeen Muhammad

 

More from Labarai