On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Jihar Kano Zata Amfan Da Sabbin Madatsun Ruwa 3 Albarkacin Shirin ACReSAL - Musa Shu'aibu

Shirin Inganta Muhalli ta hanyar amfani da sabbin dabarun Noma a yankuna masu zafi da karancin ruwan sama (ACReSAL) zai samar da dama-damai guda 3 a Kananan hukumomin Takai da Makoda da kuma Shanono domin cimma kudirin kawar da matsalolin zaizayar kasa a jihar Kano.

Shugaban shirin Alhaji Musa Shu’aibu shine ya tabbatar da hakan lokacin da jami’an shirin suka kai ziyarar ban girma ga ‘Dan majalissar sarkin Kano wato Sarkin dawaki babba, Alhaji Aminu Babba ‘Dan-agundi, ya ce a baya anyi niyyar yin aikin kawar da matsalolin zaizayar kasa da inganta madatsun ruwa karkashin shirin NEWMAP sai dai hakan bata samu ba sakamakon wasu matsaloli da rashin cika wasu ka’idoji.

Shu’aibu ya ce aikin wanda tuni gwamnatin Kano ta sanya hannu kan yarjejeniya da bankin duniya, ya kammala tsara zane da Taswirar wuraren da matsalar ta shafa kuma bankin duniya ta amince da zanen da aka gabatar amma a karkashin sabon shirin Inganta Muhalli ta hanyar amfani da sabbin dabarun Noma a yankuna masu zafi da karancin ruwan sama ACReSAL.

Ya baya ga Dama-damai da za’a samar akwai wasu ayyukan na kawar da zaizayar kasar a Kauyen Alu dake karamar hukumar Traauni da Rarin dake Dawakin Tofa da kuma Kamanda dake karamar hukumar ‘Kiru sannan akwai unguwanni Gama da Kaura Goje dake karamar hukumar Nasarawa sai ayyukan titi a Bulbula Gayawa da Tudun Fuladi a karamar hukumar Ungogo za su amfana da ayyukan da aka tsara.

Yace gidajen mutane da cibiyoyi da makabartu da saurana muhimman wuraren amfanin jama’a na cikin barazana a yankunan da aka gudanar da bincike saboda haka shirin zai taimaka wajen inganta hanyoyin noma da yadda za’a fahimci kalubalen sauyin yanayi da dabarun da za’a koyawa mutane domin cigaba da Noma da zamantakewa a junansu ba tare da matsalar tasirin sauyin yanayi ba.

Da yake nasa jawabin, Dan majalissar sarki Sarkin dawaki babba, Alhaji Aminu Babba ‘Dan-agundi, ya bukaci sabuwar gwamnati mai jiran gado a jihar Kano ta duba muhimmanci da alfanun shirin na Inganta Muhalli ta hanyar amfani da sabbin dabarun Noma a yankuna masu zafi da karancin ruwan sama wato Kano ACReSAL domin samun Nasarar da aka sa a gaba.

Haka kuma sarkin dawaki babba ya yi kira ga masu unguwanni da Dagatai da sauran al’umma su bada hadin kai ga shirin da nufin cin moriyar alfanun aikace-aikacen da za’a gudanar.

Ya kuma yabawa gwamnatin Kano bisa tallafawa shirin ta dukannin hanyoyin da ake bukata tare da Addu’a da kuma fatan samun Nasara.