On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Jiragen Yakin Rundun Sojin Sama Ta Kasa Sunyi Luguden Wuta Kan 'Yan Ta'adda A Jihar Kaduna

Jiragen Yakin Rundunar Sojin Sama ta Kasa

Yan fashin daji na cigaba da shan matsi daga bangaren rundunar sojin sama ta kasa, a yayin da rundunar ta samu nasarar lalata wasu daga cikin maboyar ‘yan fashin dajin dake kananan hukumomin Chikun da Igabi na jihar Kaduna.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan tsaro na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya fitar a ranar Litinin, Inda ya baiyana cewa, Rundunar sojin sama ta kasa, ta kai jerin hare-hare ta sama kan maboyar  yan bindiga dake wurare daban daban, a yankin Kawara dake cikin karamar hukumar Igabi.

Ya kara da cewa an halaka wasu  ‘yan bindiga Ukku a yayin sumamen, sannan kuma wadanda aka yi garkuwa dasu, sun yi amfani da damar wajen kubucewa daga  hannun  yan bindigar.

Kazalika rundunar sojin sama ta kasa, ta kaddamar da makamancin wannan sumame a yankuna Faka da Kongon Kadi, sai Damba da Ungwan Turai sai Galbi da Gwagwada, inda nan ma aka halaka wasu  ‘yan ta’addar masu yawan gaske.