On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Jude Bellingham Ya Lashe Kyautar Dan Wasan Da Ya Fi Zura Kwallaye

JUDE BELLINGHAM

Gwarzon dan wasan real Madrid da kuma kasar Ingila Jude Bellingham ya lashe kyautar gwarzon dan wasan da ya fi zura kwallaye a raga ta Kopa Trophy.

Yayin da mai tsaron raga  na kasar Argentina  Emiliano  Martinez  ya  zama  gwarzon mai tsaron raga na duniya.

 

Shi kuwa, Tauraron dan  wasan kwallon kafar  Argentina  da kuma  duniya baki daya, Lionel Messi  ya sake lashe  kyautar  gwarzon dan wasan duniya ta Ballon d’or, wanda  hakan yasa ya  sake lashe kyautar a karo na takwas, tun bayan da kasarsa  ta samu nasarar  daga  kofin duniya a shekarar  2022.

Messi dan shekara 36 a duniya  ya doke  Karim  Benzema  wajen samun  kyautar  bayan da aka gwada kwazonsu na kakar  wasannin data  gabata,  a  lokacin da  Messin ya kai Argentina ga daukar  kofin kwallon kafa na duniya.

Kazalika  itama  Aitana Bonmati  daga kasar Andalu  ita  ce  gwarzuwar  yar wasan kwallon kafar  mata  ta duniya, inda  ta cinye  kyautar ta Ballon d’or a bangare mata.

Bonmati  ta doke  abokiyar karawarta  Alexia Putellas  wajen samun kyautar.