On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Juyin Mulkin Gabon Ya Tabbatar Da Tsoron Da Mukeyi Tun Bayan Kifar Da Gwamnati A Nijar -Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce Fargabar da ya ke yi kan matsalar juyin mulki a Nijar wanda ya kafa mummunan tarihi a fadin Nahiyar Afirka ya tabbata ta hanyar hambarar da Shugaba Ali Bongo na Gabon.

Ya tabbatar da hakan ne a jiya  Alhamis yayin da yake karbar bakwancin majalisar koli ta harkokin addinin musulunci ta Najeriya karkashin jagorancin mai alfarma sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na  III a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Tinubu ya dage cewa duk wani yunkuri na kawar da gwamnatin dimokaradiyya ya kasance abunda ba za’a lamunta ba.

Ya kara da cewa Najeriya ta kafa kwamitin  mika mulki na watanni tara a shekarar 1998 kuma ta samu nasara sosai, yana mamakin dalilin da ya sa ba za a iya yin irin wannan a Nijar ba, idan har hukumomin soji na da gaskiya.