On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Kamfanoni 12 A Kano Sun Samu Takardar Ingancin Kayyaki Daga Gwamnatin Tarayya

Hukumar kula da ingancin kayayyaki ta Kasa SON ta bada takardar shedar tabbatar da Inganci ga wasu rukunin kamfanoni 12 a jihar Kano.

Da yake jawabi a wajen bikin bayar da shaidar Ingancin kayayyaki guda 25 na kamfanonin 12, babban daraktan hukumar ta SON, Malam Faruk Salim, ya gargadi wadanda suka samu takardar shiadar cewa za a iya karbe takardar idan suka saba ka’idojin hukumar.

Shugaban wanda ya samu wakilcin, Daraktan hukumar ta SON na yankin Arewa maso Yamma, Albert Wilberforce, ya bukaci sauran kamfanoni da su shiga cikin tsarin tabbatar da inganci don amfanin cigaban  kasuwancinsu.

Ya kuma bukaci jama’a da su rika amfani da kayayyakin da hukumar SON ta tabbatar da Ingancin su.

A nasa bangaren, Babban Jami’in hukumar SON na jihar Kano dake kula da offish na daya na hukumar, Qazeem Mohammed Yahaya, ya ce tsarin ba da takardar shaidar yana da tsauri don tabbatar da aminci da inganci, amma bai kamata a yiwa  hakn gurguwar fahimta ba ko kallon hukumar amatsayin wadda bata da dadin sha’ani ko mu’amala da masana’antun.