On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Kananan Yara Milliyan 1 Da Dubu 'Dari Biyar Na Cikin Hatsari A Najeriya - UNICEF

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce sama da yara miliyan 1 da dubu dari 5 a Najeriya na fuskantar barazanar kamuwa da cututtuka sanadiyar matsalolin ruwa da rashin abinci mai gina jiki yayin da ambaliyar ruwa ta afkawawa sama da jihohi 20 daga cikin 36 na kasar.

A cikin wata sanarwa da aka  fitar, Asusun  UNICEF ya ce sama da mutane miliyan 2.5 a Najeriya na bukatar agajin jin kai, inda kashi 60 cikin 100 suka kasance yara yara ne.


 Sanarwar ta kara da cewa, a sakamakon haka, kamuwa da cutar gudawa da sauran cutuka na ruwa da  cututtukan fata sun fara karuwa. 

Ya kara da cewa a jihohin Borno da Adamawa da Yobe da ke arewa maso gabas kadai, an samu jimillar mutane 7,485 da suka kamu da cutar kwalara da kuma mutuwar mutane 319 a ranar 12 ga watan Oktoba.

 

Sako Daga Arewa Radio: Taron Ina Mafita Na 2022 Zai Tattauna Kan Makomar Najeriya