On Air Now

Off Air

Noon - 6:00pm

Kanfanonin Jiragen Sama Sunki Saka Hannu Kan Yarjejeniyar Dake Tsakaninsu Da Hukumar Aikin Hajji Ta Kasa

Kanfanonin jiragen sama na cikin gida da suka hada da Air Peace da Azman da Max Airn da kuma Aero sunki saka hannu kan yarjejeniyar dake tsakaninsu da hukumar aikin hajji ta kasa kan jigilar maniyyata aikin hajjin bana sakamakon rikicin da ake yi a kasar Sudan.

A  yanzu  haka an  dage  lokacin saka  hannun kan yarjejeniyar  zuwa  ranar  Talatar  makon a  yayin da  wakilan  kanfanonin jiragen  saman suka  nemi a  basu lokaci  domin tuntubar  na  gaba  da su.

Sun yi ikirarin cewar  Sararin samaniyar  kasar  Sudan wanda  aka rufe shi saboda  yakin da ake yi a  kasar, zai  shafi  jigilar  maniyyata aikin hajjin bana da suka taso  daga yankin kasashen sahara,  kasancewar  dole  ne sai an ratsa  ta sararin samaniyar  kasar  kafin  a shiga  kasar  saudiyya, muddin ba hanya  aka  sauya  ba.

Sake  yarjejeniya tsakanin kanfanonin jiragen  saman da kuma  Hukumar aikin hajji ta kasa  zai sa  dole  sai dai  a bi  ta  wata  kasar  maimakon ratsawa  da sararin samaniyar  sudan, wanda  hakan zai kara yawan kudin aikin hajjin  da  Alhazai  zasu biya.

A  wani bangaren kuma  wani kanfanin jirgin sama  dan kasar waje  na  Fly Nas  ya saka hannu  kan yarjejeniyar  jigilar Alhazan  Najeriya  dubu 28, wanda  yake wakiltar  kaso 40 bisa 100  na  Alhazan  da zasu je aikin hajjin bana.