On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Karancin Masara Na Neman Durkusar Da Kiwon Kaji A Najeriya

Kungiyar masu kiwon kaji a Najeriya ta ce wuraren kiwon kaji na rufewa saboda cigaba da fuskantar tsadar farashin masara.

 

Masara babban bangare ne, wanda ya ƙunshi kashi 60 zuwa kashi 70 cikin ɗari na abincin kaji.

Kungiyar, a cikin wata sanarwa da shugabanta na kasa, Sunday Ezeobiora, ya fitar, ta ce masana’antar  kiwon kaji a Najeriya na gab da rushewa gaba daya idan gwamnati ba ta yi gaggawar shiga cikin al’amarin ba.

Rahotanni sunce, saboda matsalar, farashin ƙwai, wanda shine tushen sinadarin furotin ga ƴan Najeriya da dama, ya yi tashin gwauron zabi da sama da kashi 118.34 cikin ɗari bayan da aka samu koma bayan na yawan shigo da masara da kashi 97.91 cikin ɗari.